Kinnear ya raba gari da Newcastle

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Joe Kinnear

Joe Kinnear ya yi murabus a mukaminsa na darektan kwallon kafa a Newcastle kasa da watanni takwas da karbar mukamin.

Dan shekaru 67, yana a saman kocin kungiyar Alan Pardew a tsarin kulob din saboda shi ne keda alhaki daukar 'yan wasa.

A karkashin mulkinsa, kungiyar ba ta sayi wani dan kwallo ba sai dai sayar da wasu.

A ranar Asabar, Pardew ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda kungiyar ta kasa sayen sabbin 'yan kwallo, bayan ta sha kashi a wajen Sunderland a gida.

Newscastle ta sayar da Yohan Cabaye ga Paris St-Germain a kan fan miliyan 19 a watan da ya wuce amma kuma ba ta maye gurbinsa ba.