Swansea ta kori Micheal Laudrup

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Micheal Laudrup

Kungiyar kwallon kafa ta Swansea City ta kori kocin tawagartsa Michael Laudrup inda kyaftin din kungiyar Garry Monk zai ja ragamar.

Shugaban kungiyar Huw Jenkins ya ce ya dauki matakin ne don kawo karshen matsalar da kungiyar ke fuskanta.

Swansea ta sha kashi a wasanni shida cikin takwas, inda a yanzu maki biyu ne ya raba ta da kungiyoyi dake rukunin wadanda za su iya komawa rukunin championship.

Baya da Laudrup an kuma kori wasu daga cikin mataimakansa.

Karin bayani