Vela ba zai buga gasar kofin duniya ba

Carlos Vela Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya yanke ba zai bugawa Mexico wasa ba

Hukumar kwallon Mexico ta sanar da cewa Carlos Vela baya cikin 'yan wasan da za su buga mata gasar kofin duniya da za a fafata a Brazil a bana.

Dan wasan mai shekaru 24 ya zura kwallaye 10 a Real Sociedad a kakar bana, amma rabonsa da bugawa kasarsa wasa tun a shekarar 2011.

Tsohon dan kwallon Arsenal an sanar da cewar ba zai buga kofin duniya ba a shekarar 2014 da hukumar kwallon Mexico ta sanar da cewa "Vela ya ce bai shirya bugawa Mexico wasa ba."

Kocin Mexico Miguel Herrera, da daraktan wasan kungiyar kasar Hector Gonzalez da jami'an hukumar sun ziyarci dan wasan a Madrid ranar Litinin domin tattaunawa da shi.

Dan wasan ya zura kwallaye tara a raga a wasanni 35 da ya bugawa Mexico, daga baya suka samu rashin jituwa tsakaninsa da hukumar kwallon kasar a shekarar 2011.

Mexico za ta fara karawa da Kamaru a rukuni na farko ranar 13 ga watan Yuni a kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci a bana.