Beckham zai kafa kungiya a Amurka

David Beckham Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Beckham na fatan kungiyar zata yi fice a duniyar kwallo

Tsohon Kyaftin din Ingila David Beckham na shirin kaddamar da sabuwar kungiyar kwallon kafa a Miami da za ta kara a gasar MLS.

Kungiyar za ta zamo ta farko a birnin Florida tun bayan shekarar 2001.

Amincewa da Beckham ya yi na sayan kungiya a Amurka, ana hangen yana cikin yarjejeniyar da ya kulla da LA Galaxy a lokacin da ya koma kungiyar a 2007.

Beckham mai shekaru 38, tsohon dan kwallon Manchester United da Real Madrid da AC Milan da Paris St-Germain mai wasan tsakiya ya yi ritaya ne dai a Mayun bara.