Cape Verde ta ba da hujja —kotu

Image caption Kotun ta ce Cape Verde ba ta da madogara

Kasar Cape Verde ta sha kaye a karar da ta kai saboda hana ta zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a bana.

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, FIFA, ce dai ta hana Cape Verde gurbin zuwa gasar, lamarin da ya sa kasar ta shigar da kara a kotun da ke shari'a kan harkokin wasanni.

Cape Verde, wacce ta buge Tunisia da ci 2-0 kuma ta zama ta farko a rukunin B na kasashen Africa, ta kauracewa wasan bayan Fifa ta yi hukuncin cewa dan wasanta, Fernando Varela , bai cancanci buga wasan ba.

An dai bai wa Tunisia nasara kan Cape Verde da ci 3-0 , lamarin da ya sa 'yan wasan Tunisian suka kasance a gaba a cikin rukunin; kuma suka buga wasan fid-da-gwani a madadin Cape Verde.

Kotun dai ta ce karar da Cape Verde ba ta da madogara.

Karin bayani