Wigan ta dauki Markus Holgersson

Markus Holgersson Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasa na biyar kenan da yazo kungiyar

Wigan ta dauki mai tsaron baya Markus Holgersson, wanda yarjejeniyarsa ta kare da New York Red Bulls ta Amurka a watan Janairu.

Mai shekaru 28 ya bugawa Sweden wasanni, sannan ya bugawa a gasar Amurka karo 67, da ya taka leda tare da tsoffin 'yan wasan Premier Thierry Henry and Tim Cahill.

Tsohon dan kwallon Helsingborgs mai tsaron baya Holgersson, shine dan wasa na shida da ya koma DW, kafin shi akwai Tyias Browning da Nicky Maynard da Josh McEachran da Martyn Waghorn da suka koma kungiyar.

Kocin kungiyar Uwe Rosler ya ce a 'yan wasan baya suka fi samun matsala, saboda haka zuwan Markus zai karawa kungiyar kwarin gwiwa.