Djemba-Djemba na harin buga kofin duniya

Djemba-Djemba Hakkin mallakar hoto sns
Image caption Dan wasan zai sa kaimi domin buga kofin duniya

Sabon dan kwallon St Mirren Eric Djemba-Djemba na fatan samun damar bugawa Kamaru kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci a bana.

Djemba-Djemba wanda kungiyarsa Partizan Belgrade ta amince ya koma wata kungiyar, bayan watanni shida da ya buga mata wasanni a yarjejeniya shekaru biyu, ya kulla gajeriyar kwantaragi da Paisley .

Dan wasan mai shekaru 32, ya bugawa kasarsa wasanni 24 ya kara da cewa "Ina fatan kocin Kamaru zai ga wasana a sabuwar kungiyar dana koma, sannan ya gayyace ni buga kofin duniya a Brazil."

Djemba-Djemba baya cikin 'yan kwallon da koci Volker Finke ya ke amfani da su wajen bugawa Kamaru wasanni.