Ethiopia ta kori kocinta Bishaw

Sewnet Bishaw
Image caption Wasanni ne suka kwacewa kocin a watan baya

Hukumar kwallon Ethiopia ta kori kocin tawagarta Sewnet Bishaw saboda kasa taka rawar a lokacin gasar cin kofin Afrika a Afrika ta Kudu.

An doke Ethiopia a wasannin uku a zagayen farko na gasar 'yan kwallon dake taka leda a cikin nahiyar.

Shugaban hukumar, Juneidin Basha ya shaidawa BBC cewar kocin ya yi abun kunya.

Bishaw ya jagoranci kasar zuwa kofin Afirka karon farko bayan shekaru 31 da suka halarci wasan da Afirka ta kudu ta karbi bakunci a bara.

Ya kuma kai wasan cike gurbin shiga gasar kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci a bana, amma ya yi rashin nasara a hannun Najeriya da ci 4-1 a jumullar wasan da suka kara.

Sai dai kuma rashin nasarori a watannin baya yasa ya rasa aikinsa.

Hukumar kwallon Ethiopia EFF ba ta sanar da wanda ya maye gurbinsa ba, sai dai ana ganin hukumar zata nemo mai horas wa daga waje.