'Liverpool ba za ta iya lashe gasa ba'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Brendan Rodgers na kokarin shiga gaban Spurs da United

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce kungiyarsa ba za ta iya lashe gasar Premier ta bana ba.

A kakar wasan da ta wuce Liverpool ce ta bakwai a kan tebur sannan a yanzu haka ita ce ta hudu a kan tebur, inda Arsenal ke gabanta da maki takwas.

Rodgers yace "Ba na kallonmu a matsayin wadanda za su iya lashe gasar bana, amma dai ya yi wuri a tantance".

Sai dai kuma tsohon kocin Swansea din ya ce kungiyarsa za ta iya karkewa cikin manyan kungiyoyi hudu na farko a gasar ta Premier a bana.

A ranar Asabar, Liverpool za ta dauki bakuncin Arsenal a wasan da ake gannin zai yi zafi.

Karin bayani