"Draxler zama daram a Schalke"

Julian Draxler Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan zai kara shekara daya a Schalke ta Jamus

Shugaban kungiyar Schalke Clemens Tonnies ya ce mai wasan tsakiya Julian Draxler baya sha'awar komawa Bayern Munich.

Dan kwallon mai shekaru 20, wanda aka dangata shi da komawa Arsenal a watan Janairu, zai iya barin kungiyar kan kudi £38m.

Clemens Tonnies a hirar da aka yi da shi a mujallar Bild ya ce "Duk kungiyar da ta bukaci daukar dan wasan a nan gaba zamu amince ya tafi, hakan munyi masa adalci."

"Bana jin idan yana son komawa Bayern Munich," in ji Tonnies.

Shugaban wanda yaki barin dan wasan yabar kungiyar a bana da ba'a bayyana kungiyarba, yana kokarin ganin dan kwallon Jamus ya sake bugawa Schalke wasa a kakar bara.