Laudrup zai kai Swansea kotu

Michael Laudrup Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin na jiran jin dalilan da yasa aka kore shi

Michael Laudrup ya ce zai kai Swansea kara a kotu bayan da kungiyar ta sallame shi daga aiki a ranar Talata.

Dan kasar Denmark wanda ya jagoranci Swansea ta lashe gasar 'League Cup' a bara, ya ce ba a barshi ya dawo filin atisaye ba domin yin ban kwana da 'yan wasa ba.

A wani jawabi da ya yi wa hukumar gudanar da gasar Premier LMA, Laudrup ya ce har yanzu yana jiran yaji dalilan da yasa kungiyar ta sallame shi.

"Hukumar gudanar da gasar Premier LMA ta rubutawa kungiyar neman dalilan da yasa kungiyar ta sallame ni," in ji Laudrup.