Hazard na son ya kamo Messi da Ronaldo

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Eden Hazard

Dan kwallon Chelsea Eden Hazard ya ce yanason ya kai matsayin irinsu Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a fagen kwallon kafa a duniya.

Dan wasan kasar Belgium din yana haskakawa a kakar wasa ta bana inda ya zura kwallaye 11 cikin wasanni 34.

Hazard yace "A duniya babu 'yan kwallo kamar Messi na Barcelona da kuma Ronaldo na Real Madrid".

Hazard, wanda ya koma Chelsea daga Lille a shekara ta 2012 a kan fan miliyan 32 ya ce "Ina maida hankali sosai wajen horo don cimma burin kaiwa kamarsu".

Yana kallon kansa a matsayin daya daga cikin zaratan 'yan kwallo a duniya.

Karin bayani