Johnson ya samu kyautar watan Junairu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau biyu Hodgson ya gayyaci Adam Johnson

An baiwa dan kwallon Sunderland Adam Johnson kyautar gwarzon dan wasan Premier na watan Junairu.

Johnson mai shekaru 26, ya zura kwallaye biyar a cikin wasanni hudu da ya buga wa kungiyar a cikin watan da ya wuce.

Haskakawarsa ta sa wasu sun soma ganin ya kamata kocin Ingila Roy Hodgson ya gayyace shi cikin tawagar 'yan kwallon kasar da za ta buga a gasar cikin kofin duniya a Brazil.

Haka kuma an baiwa kocin Manchester City, Manuel Pellegrini kyautar gwarzon koci na watan Junairu.

City ta zura kwallaye 14 cikin wasanni hudu a watan da ya wuce.