Vidic zai bar Manchester United

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Nemanja Vidic ya yi fama da rauni a 'yan shekarunnan

Kyaftin din Manchester United Nemanja Vidic zai bar kungiyar a karshen kakar wasa ta bana.

Dan kasar Serbia mai shekaru 32, wanda ya soma taka leda a Old Trafford a shekara ta 2006, yarjejeniyarsa za ta kare da kulob din a watan Yunin bana.

Vidic yace" Ba zan ci gaba da taka leda a Ingila ba, don na yanke shawarar koma wa wata kasa don murza leda".

Vidic ya koma United ne daga Spartak Moscow a kan fan miliyan 7 kuma ya lashe kofuna da dama tare da kungiyar.

Ya taimakawa Manchester United ta lashe gasar zakarun Turai a shekara ta 2008 sannan ya buga wasannin Premier 201 cikin shekaru takwas.

Karin bayani