"Doke mu da liverpool ta yi ya kawo shakku"

Arsene Wenger
Image caption Wenger na hangen komawa matsayi na daya a teburi

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya jaddada cewa Gunners za ta iya lashe kofin Premier, amma gannin Liverpool ta doke su 5-1 ranar Asabar ya kawo shakku a kan kokarin 'yan wasan kungiyar.

Gunners ta kara da Liverpool a lokacin tana ja gaba a teburin Premier, sai kuma Liverpool ta doke Arsenal a Anfield.

'Yan wasan Wenger za su karbi bakuncin Manchester United a filin Emirates ranar Laraba a kofin Premier wasan mako na 26.

Wenger ya ce "An sa shakku da ke bukatar mu kawar da shi daga magoya bayanmu ranar Laraba. Har yanzu ina hangen zamu iya lashe kofin Premier a bana."

Doke Arsenal 5-1 a Anfield shi ne karo na hudu a tarihin gasar Premier da aka zura wa kungiyar kwallaye biyar ko sama da haka a wasa guda kuma karo na biyu a bana.

Cikin minti 20 aka zura kwallaye hudu a ragar Arsenal a karawar da ta yi da Liverpool.