"Ban ji dadin buga diro da Norwich ba"

Manuel Pellegrini Hakkin mallakar hoto AP
Image caption City ta dawo matsayi na uku a teburin Premier

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini bai ji dadin tashi wasa babu ci a karawar da suka yi da Norwich a kofin Premier, ya kuma kare kungiyar kan rashin zura kwallo a wasa biyu a jere.

City ta kafa tarihin zura kwallaye 68 bayan buga wasanni 23, sai dai Chelsea ta doke ta daci daya mai ban haushi kafin ta buga diro da Norwich a filin Carrow Road

Pellegrini yace "Yan wasana masu zura kwallo a raga da suka hada da Edin Dzeko da Alvaro Negredo basu da koshin lafiya."

Ya kuma kara da cewa "Kowacce kungiya zata barar da maki, kuma Chelsea ta bamu tazarar maki biyu amma a kwai maki 39 da zamu yi kokawar lashe wa."

Bayan da Chelsea ta doke City a Etihad ranar Litinin ta kuma casa Newcastle daci 3-0 ranar Asabar hakan yasa ta dare teburin Premier ta kuma bai wa Arsenal da aka doke 5-1 a hannun Liverpool tazarar maki daya sai City a matsayi na uku a teburin Premier.