United da Fulham sun buga 2-2

United Fulham Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption United tana matsayi na bakwai Fulham ta 20 a teburi

Kungiyar Manchester United ta tashi wasa da Fulham 2-2 a kofin Premier wasan mako na 25.

Fulham ce ta fara zura kwallo ta hannun Steve Sidwell.

Daga baya kungiyar ta koma tsare bayanta, sai dai United ta farke kwallo ta hannun Robin Van Persie sannan Michael Carrick ya kara kwallo ta biyu.

Kace haka wasan za a tashi, nan take dan wasan Fulham Kieran Richardson ya samu kwallo ya buga wa golan United David De Gea shi kuma ya buge kwallo amma Darren Bent ya kai ga samata kai ta kuma shiga raga.

United tana matsayi na bakwai a teburi da maki 41, ita kuwa Fulham nada maki 20 a matsayi na karshe a teburin Premier.