An kashe mai goyon bayan Liverpool a Kenya

Image caption 'Yan Liverpool sun jikawa Arsenal gari

'Yan sanda a Kenya na neman wani mutumi da ake zargin ya kashe wani mai goyon bayan Liverpool da wuka, bayan wasa tsakanin Arsenal da Liverpool a ranar Asabar.

Mazauna yankin sun ce mutumin da yayi kisan yana goyon bayan Arsenal ne, kuma bayan da Liverpool ta lallasa Arsenal daci biyar da daya sai ya aikata ta'asar bayan sun gama kallon kwallo a gidan kallo dake garin Meru a kasar ta Kenya.

Shaidu sun ce mai goyon bayan Arsenal din ya fitar da wuka sai ya cakawa dan Liverpool din wanda ya mutu jim kadan a asibiti.

Dubban 'yan kasar Kenya na bin gasar Premier ta Ingila sau da kafa.

'Gidajen kallon kwallo'

Image caption Kocin Liverpool, Branden Rodgers ya jinjinawa 'yan kwallonsa

Wakiliyar BBC Angela Ngendo ta ce Nairobi babban birnin Kenya na cike da gidajen kallo masu yawa, kuma jama'a na shiga a lokutan manyan wasanni.

Shugaban 'yan sanda a Meru, Tom Odero ya shaidawa BBC cewar ba zai iya tantance manufar wannan mutumin da ake zargi da kisa ba, har sai an kama shi.

A bara ne wani mai goyon bayan Manchester United a Kenya ya kashe kansa, bayan United ta sha kashi a hannun Newcastle United.

A shekara ta 2009, wani mai goyon bayan Arsenal ya rataye kansa bayan kungiyarsa ta sha kashi a wajen Manchester United.

Karin bayani