"Surutai ne ke kashe karsashin Messi"

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan zai dawo ganiyarsa a kakar bana

Kocin Barcelona Gerardo Martino ya ce surutai da zargi mara amfani ne suka dasashe kokarin Lionel Messi bisa kwazon da yake nuna wa a bana.

Zakaran kwallon duniya sau hudu ya zura kwallon a wasan da suka doke Sevilla 4-1 ranar Lahadi, kuma rabonsa da zura kwallo tun a Satumbar bara.

Martino ya ce "Masu sukan dan wasan mara amfani basu san hakan yana shafar wasanninsa ba."

Dan kwallon Argentina ya gamu da rauni a kakar wasan bana da ya zauna jinya watanni biyu, a yayinda da kuma ya samu sauki ya kasa zura kwallo a wasanni ukun farko da ya buga kafin ya zura kwallo a dokewar da Valencia ta yi musu daci 3-2 a Fabrairu.