Raja Casablanca ta lashe Diamond Stars

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Raja Casablanca ce ta biyu a gasar zakarun duniya 2013

Raja Casablanca ta Morocco ta lallasa Diamond Stars ta Sierra Leone 6-0 a wasan farko na gasar zakarun Afrika.

Raja, wacce ta buga wasan karshe na zakarun kwallon kafa na duniya da Bayern Munich a watan Disamba ta samu nasarar ne bayan da Mouhssine Iajour ya zura kwallaye hudu sannan Abdullahi Hafidi da Abdelkabir El Ouadi su ka jera dai daya.

Kungiyar Young Africans ta Tanzania ce ta samu nasara mafi girma a wasannin da aka buga a makon farko na gasar, inda ta ragargaji Komorozine Sports ta Comoros Islands 7-0.

Al Ahly Benghazi ta Libya ma ta samu nasarar 4-0 kan Foullah Edifice ta kasar Chad.