Enyimba ta doke Ange de Notse 3-1

Image caption 'Yan wasan Enyimba

Daya daga cikin kungiyoyi biyun da ke wakiltar Nigeria a gasar cin kofin kwallon kafa ta zakarun Afrika, Enyimba ta yi nasarar 3-1 akan takwararta ta Togo Ange de Notse, yayinda takwararta Kano Pillars ta sha kaye 3-1 a hannun AS Vita ta jamhuriyar dimokradiyyar Congo.

Enyimba, wacce ta lashe gasar sau biyu a baya ta mamaye 'yan Togon a wasan da su ka buga a filin wasanta da ke Aba, Nigeria.

Asante Kotoko ta Ghana ma ta samu nasara kan Barrack Young Controllers ta Liberia 2-1, yayin da daya kungiyar ta Ghana, Berekum Chelsea ta doke Atlabara ta Sudan ta Kudu 2-0.

Sai dai wakiliyar jamhuriyar Nijar, AS Douanes wacce ta shiga gasar a karo na farko ta sha kaye ne 2-0 a wurin Zamalek ta Egypt.