Mourinho ya bukaci a hukunta Toure

Yaya Toure Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan wasan na jiran hukuncin da FA za ta yanke

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce ya kamata a dakatar da dan kwallon Manchester City Yaya Toure wasanni, bayan da aka ga alamar ya tokari dan kwallon Norwich, Ricky van Wolfswinkel.

Toure, mai shekaru 30, zai iya fuskantar dakatarwar wasanni uku a karawar da suka tashi wasa babu ci a filin Carrow Road.

Mourinho yace "idan har ba a dakatar da shi ba to sakon a bayyane yake cewa zaka iya abinda kaga dama, amma idan FA tana son kare martabar kwallo to ya kamata a dakatar da shi".

Hukumar FA na jiran rahotan alkalin wasa Jon Moss.