West Ham za ta sayarda Upton Park

Upton Park
Image caption Tun a 1909 West Ham ta fara wasa a Upton Park

West Ham ta cimma yarjejeniyar sayar da filin wasanta Upton Park ga wani kamfanin gine-gine Galliard Group, da zarar ta koma filin wasan Olympics a shekara ta 2016.

Hammers ta ce ta amince da sayar da filin ne ganin yadda kamfanin yake mahada da al'umma.

Mataimakin shugaban kungiyar Karren Brady ya ce West Ham ta cika alkawarin da ta dauka na habbaka cibiyoyi biyu daga yammacin Landan.

Kamfanin da zai sayi filin yana shirin gina sabbin gidajen haya da shaguna da wuraren shakatawa nan da 2018.

Hammers ta fara wasan farko a filin a shekarar 1909, sunan da aka radawa filin shi ne Boleyn Ground amma an fi kiransa da Upton Park dake cin 'yan kallo 35,000.

Haka kuma ana tattaunawa da iyalan tsohon dan wasan West Ham da Ingila kyaftin Bobby Moore a kan damar ware wani lambu da za'a amsa sunan dan wasan da butun- butuminsa.