"Za mu tattauna kan zaman Barry a Everton"

Roberto Martinez
Image caption Kocin yace sai karshen kakar bana za su zauna kan dan wasan

Kocin Everton Roberto Martinez ya ce kungiyar ba za ta tattaunawa kan zaman Gareth Barry a kungiyarba har sai nan da karshen kakar wasan bana.

Barry, dan shekaru 32 mai wasan tsakiya yana zaune ne a kungiyar a matsayin aro daga Manchester City kuma kwangilarsa za ta kare a karshen kakar wasan bana.

Ana danganta Arsenal da dan wasan Ingilan.

Martinez yace "Ina ganin fitaccen dan wasan Ingila ne babu dan kwallon da yafi shi fice a gurbin da yake buga wasa, kuma manyan kungiyoyi za su bukaci daukar dan wasan."

Barry ya bugawa Everton wasanni 20 a kofin Premier bana, yana daga cikin 'yan kwallon da suke saka kaimi na ganin kungiyar ta kare a 'yan biyar din farko.