Za a soma fara wasa da Lacina a Everton

Lacina Traore Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya shirya fuskantar kalubalen Premier

Dan kwallon Ivory Coast Lacina Traore na daf da bugawa Everton wasan farko a karawar da za suyi da Crystal Palace ranar Laraba.

Mai shekaru 23, ya koma kungiyar ne dai a watan jiya daga Monaco ta Faransa a matsayin aro.

Everton ta dauki dan wasan yana da rauni, kuma tun a lokacin koci Roberto Martinez ya sanar ta yanar gizon kungiyar cewa "bana tsammanin dan wasan zai buga mana wasa domin yana jinya.

"Ina hangen zai buga mana karawar da za mu yi da Crystal Palace, amma ba zai iya buga cikakken wasa ba," in ji Martinez.

Dan mai tsawon kafa 6 da inci 8 ya zauna a benci ranar Lahadi a karawar da Tottenham da dake su da ci daya mai ban haushi.

Everton tana matsayi na 6 a teburin Premier, kuma Liverpool dake matsayi na hudu ta bata tazarar maki biyar a kokarin neman gurbin buga kofin zakarun Turai.