Pellegrini bai iya kirge ba — Mourinho

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin suna mai da magana tsakanisa da Pellegrini

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce Manuel Pellegrini bai gane lissafin kudaden musayar 'yan wasa da Chelsea tayi a Janairu ba.

Mourinho ya kwatanta kungiyar da dan karamin dokin sukuwa a lashe kofin Premier, yayin da Pellegrini yace Chelsea dokin sukawa ne mai tsada.

Kocin Chelsea yace "Mun sayar da Mata kan kudi £37 miliyon da De Bruyne kan kudi £18 miliyan, jumulla kudi £55 miliyan."

Ya kara da cewar "Mun sayo Matic kan kudi £21 miliyan da Salah kan kudi £11 miliyan, mun samu rarar kudi £23 miliyan kenan."

Mourinho ya kara da cewa "muna hada 'yan wasa domin tunkarar gasar wasanni masu zuwa, amma City tuni ta hada 'yan kwallon da za su lashe kofuna."

Chelsea na kan gaba a teburin Premier da maki guda bayan data doke Newcastle ranar Asabar. Arsenal na biye a matsayi na biyu sai City ta uku da Chelsea ta bata tazarar maki biyu.