Newcastle ta bukaci Cisse ya kara kwazo

Papiss Cisse
Image caption Dan kwallon na daf da dawowa wasa bayan jinya da ya yi

Makomar dan kwallon Senegal Papis Cisse a Newcastle tana reto.

Dan wasan mai shekaru 28 ya shiga kungiyar ne a shekarar 2012 ya kuma zura kwallaye 13 a wasanni 14 da ya fara bugawa kungiyar wasa.

Koci Alan Pardew ya kalubalanci dan wasan da ya kara saka kaimi ko kuma kungiyar ta sayar da shi.

Kocin ya kara da cewa "Zamu nemi mafuta akan dan wasan, idan zai maida hankali ya dawo cikin manyan 'yan wasan kungiyar kamar yadda yayi a shekaru biyu baya ko kuma sayar da shi za mu yi".

Cisse ya zura kwallaye uku a wasanni 18 a kakar wasan bana, kuma yana bayan Loic Remy da kungiyar ta dauko aro daga QPR a yawan zura kwallo.

Biyu daga kwallayen da ya zura na daga cikin wasanninsa uku na karshe da ya buga kafin ya tafi jinya a raunin da ya ji a sansanin horo a Abu Dhabi a watan jiya.

Dan wasan na daf da dawowa daga jinya, ya kuma rage gare shi ya kara kaimin wasanninsa ganin yaci gaba da bugawa kungiyar kwallo.