Yaya Toure ya tsallake hukuncin FA

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yaya Toure

Dan wasan Manchester City Yaya Toure ba zai fuskanci hukunci game da abin da ya faru tsakaninsa da Ricky van Wolfswinkel na Norwich City a wasan da su ka buga canjaras ranar Asabar.

Toure mai shekaru 30 ya tsallake hukuncin dakatarwar wasanni uku bayan da kwamitin hukumar FA ya ce bai samu hujjar tuhumarsa da kwarfe dan wasan gaban na Norwich ba.

Rafali, Jon Moss dai bai shaida faruwar lamarin ba a lokacin wasan amma FA na da damar daukar hukunci bisa amfani da hotunan bidiyo.

Tuni dai van Wolfswinkle ya baiyana farin cikinsa da matsayin na FA, inda ya ce tsautsayi kan faru a filin kwallo, amma bai dace a dakatar da Toure ba.

Karin bayani