West Brom Albion ta rike Chelsea 1-1

Image caption Victor Anichebe

Dan wasan West Brom Victor Anichebe ne ya farke kwallon da ta hana jagorar Premier, Chelsea muhimmiyar nasarar da ta ke bukata a filin The Hawthorns.

Chelsea dai ta nuna alamar za ta iya ba da tazarar maki hudu a saman tebur ne bayan da Branislav Ivanovic ya zura kwallon da David Luiz ya buga masa.

Golan West Brom kuma ya kare kwallaye daga Samuel Eto'o da Willian.

Sai dai farkewar da Anichebe ya yi ta ba kungiyar damar ficewa daga matakin kasan teburin Premier.

Sannan kuma ta jawo kokwanton anya Chelsea, wacce a makon jiya ta yi canjaras da West Ham za ta iya lashe kofin Premier a bana kuwa?