West Ham ta lula a rukunin Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sam Allardyce ya yaba da kokarin yaransa.

West Ham ta hau mataki na 10 a gasar Premier bayan da 'yan wasanta James Collins da Mohammed Diame su ka jefa kwallo a ragar Norwich.

'Yan wasan Norwich uku; Gary Hooper, Robert Snodgrass da Alex Tettey ne su ka yi kokarin zura kwallo amma golan West Ham, Adrian ya tare.

Nasarar ta nuna yadda yaran na Sam Allardyce su ka farfado bayan da su ka fara wasannin karshen makon jiya a matsayi na 18 a Premier.

Tun bayan kunnen dokin da ta yi da Chelsea a Stamford Bridge ranar 29 ga Janairu, West Ham ta doke Swansea, Aston Villa da Norwich duk da nasarar 2-0.