Villa na son gwada kallon kwallo a tsaye

Villa Park
Image caption Filin wasan da suke son gwada dawo da kallon kwallo a tsaye

Kungiyar Aston Villa ta shaidawa BBC cewa yawancin kungiyoyin Premier na sha'awar dawo da kallon kwallon kafa a tsaye a filayen wasa.

Villa ta bayar da izinin gwajin wani sashen filin da 'yan kallo za su kalli wasa a tsaye.

Manajan tsare-tsare na kungiyar, Lee Preece, ya ce "Za mu yi murna matuka idan muka gwada kallon kwallon a tsaye a filinmu idan hakan zai fi alfanu.

"Mun ware wasu kananan wurare da za mu yi gwaji, ko sauran kungiyoyi za su kwaikwayemu a fagen gasar Premier."