"Mun kasa jurewa wasan West Brom"

Jose Mourinho
Image caption Kungiyar ta barar da maki biyu a karawa da West Brom

Kocin Chelsea, Jose Mourinho, ya ce kungiyarsa ta kasa jurewa a karawar da ta yi da West Brom bayan da suka rasa maki biyu a kokarin da take na lashe kofin Premier a bana.

Branislav Ivanovic ne ya fara zura kwallo, al'amarin da ya sa aka zaci Chelsea za ta kai matsayi na daya da maki hudu.

Amma daga baya dan wasan da ya shigo sauyi Victor Anichebe ya farke kwallon a minti na 87; wasa ya koma1-1.

Mourinho ya ce "West Brom ta yunkuro ne a lokacin da muka kasa jurewa."