Gerrard zai iya buga gaba - Rodgers

Steven Gerrard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rodgers ya ce tawagar Ingila za ta muri dan wasan a kofin duniya

Kocin Liverpool, Brendan Rodgers, ya ce Steven Gerrard zai bayar da gudunmawa a matsayin dan wasan gaba a tawagar Ingila.

Dan kwallon mai shekaru 33, mai wasan tsakiya a bana a Liverpool, an ba shi damar matsawa gaba da kwallo a koda yaushe.

Rodgers na fatan kocin Ingila Roy Hodgson zai bai wa dan wasan damar buga irin wannan salon wasa a gasar cin kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci.

Kocin Liverpool ya ce, "Kowa ya san kokarin dan wasan, kuma Roy ya kamata ya yi amfani da irin wannan damar".