Muna neman sa'a — Moyes

David Moyes Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyar na fama da koma baya a kakar wasan bana

Kocin Manchester United David Moyes ya ce kungiyar na bukatar sa'a da za ta sauya rashin kokarinta a kakar wasan bana.

United za ta kara da Arsenal a filin Emirates ranar Laraba wanda take matsayi na bakwai a teburi, tazarar maki tara tsakaninta da 'yan hudun farko masu neman gurbin kofin zakarun Turai.

Sun rasa maki 21 a rashin kokarin da bai kai kakar bara ba adai-dai wannan lokacin, kuma ta yi rashin nasara a wasanni biyar a kakar wasan bana ta kuma tashi Canjaras da Fulham wacce take matsayi na karshe a teburi.

Moyes yace "muna neman sa'a da za ta sauya makomarmu".