Ribar Manchester United ta karu

Manchester United
Image caption Kungiyar ta samu riba a lokacin da take samun koma baya a wasanninta a bana

Kungiyar Manchester United ta samu karin kudin shiga ta hanyar tallace-tallace da nuwa wasanninta wanda ya bunkasa mata ribarta.

Zakarar kofin Premier ta ce kudin shigarta ya karu da kashi 11.6% a farkon shekara da karin £122.9 miliyan a karshen watannin ukun shekarar 2013.

A bangaren tallace-tallace ta samu karin 18.8% dai-dai da yadda ta samu a shekarar 2012, a inda tallata wasanta ta samu karin kudin shiga da kashi 18.7%.

Kungiyar ta samu karin kudin daukar nauyi da ya yi tashin gwauron zabi zuwa kusan 40%, da kuma sabunta yarjejeniyoyi guda shida.

United ta samu karin kudin shigar ne duk da kungiyar ba ta taka rawar gani a kakar bana karkashin jagorancin sabon koci David Moyes.

Kungiyar tana matsayi na bakwai a teburin Premier kuma a karo na farko za ta kasa shiga kofin zakarun Turai wanda rabonta da kasa shiga gasar tun shekarar 1995.