"Liverpool ta zama kadangaren bakin tulu"

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto PA
Image caption kocin na hangen zai iya lashe kofin Premier a bana

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce kungiyarsa ta zama kadangaren bakin tulu a tsakanin kungiyoyin da ke rige-rigen lashe kofin Premier a bana.

Kocin ya fadi haka ne da nufin mayar da martani akan kalaman kocin Chelsea Jose Mourinho.

Mourinho yaki ya amince da cewa zai lashe kofin Premier a bana, yana mai cewa kungiyarsa kamar dan karamin dokin sukuwa ne a tseren lashe Premier.

Doke Fulham da Liverpool ta yi ranar laraba ya sa kungiyar ta koma matsayi na hudu da tazarar maki hudu tsakaninta da Chelsea wacce take matsayi na daya a teburin Premier.

Rabon Liverpool ta lashe kofin Premier tun a shekarar 1989-90, kuma Chelsea mai matsayi na daya, da Manchester City, mai matsayi na uku a teburi za su ziyarci Anfield.