Za a kara girman filin Ettihad

Ettihad Stadium
Image caption Tun farko an gina filin ne domin wasannin Commonwealth

An amince da a kara girman sashin 'yan kallon wasa na Manchester City daga 'yan kallo 48,000 zuwa 62,000.

Za a kara ginin ne ta bangaren Arewaci da Kudancin wurin da 'yan kallo ke zama.

Hakan zai sa a samu karin wurin zaman mutane 6,250 da kuma karin wurin zama daf da fili na kujeru 2,000 da za a samu.

Idan aka gama karin filin wasa na Ettihad zai zama na biyu a yawan cin 'yan kallo a gasar Premier biye da filin Manchester United Old Trafford.

An bada izinin karin wurin zaman ne dai a taron da kungiyar ta gudanar a inda kwamitin tsare-tsare ya amince da a kammala aiki kafin fara kakar wasanni ta 2015-16.

City ta koma filin ne a shekarar 2003, a lokacin ya na daukar 'yan kallo 38,000 da aka gina domin karbar bakuncin wasannin Commonwealth a shekarar 2002.