United za ta kare a na hudu- Moyes

David Moyes Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin ya ce zai saka kaimin lashe wasanninsu na gaba

Kocin Manchester United, David Moyes, ya jaddada cewa yana hangen kungiyar za ta kare a matsayi na hudu a teburin Premier na bana.

United ta tashi wasa babu ci ranar Laraba da Arsenal, kuma ta samu tazarar maki 11 a gurbin neman buga kofin zakarun Turai.

Liverpool, wacce take matsayi na hudu a teburi, ta kara tazarar maki 11 tsakaninta da United bayan da ta doke Fulham da ci 3-2 a Craven Cottage.

Moyes ya ce, "Babu wata kungiya da take alfaharin lashe wasa a yanzu da za ta firgita kungiyoyin da ke kan gaba a Premier da ya wuce United''.

"Za mu ci gaba da saka kaimi ko za mu samu mafuta, mu dai za muyi abinda ya kamata don cimma burinmu, muna so mu kara kwazo kuma ba za mu damu da sanya ido kan sauran kungiyoyi ba, za muyi kokarin lashe wasannin mu na gaba'', in ji Moyes.

Canjaras da United ta yi a arewacin London ya tsawaita buga wasanni da ba ta lashe wasa ba, da canjaras da ta yi ranar Lahadi da Fulham da kuma rashin nasara a hannun Stoke City.