Shakku game da shekarun dan Kamaru Minala

Hakkin mallakar hoto Joseph Minala
Image caption Dan kwallon Kamaru, Joseph Minala

Kungiyar Lazio ta ce za ta dauki matakin shari'a a kan wadanda ke tababa game sahihancin shekarun dan kwallonta na Kamaru, Joseph Minala mai shekaru 17.

Kungiyar ta ce takardun haihuwarsa 'bana jabu bane'.

Lazio ta ce "Muna da 'yancin yin shari'a da duk wadanda ke kokarin batawa dan kwallonmu suna".

Dan kwallon ya fitar da sanarwa inda ya karyata cewar ya fadawa wani shafin Intanet a Afrika cewar shekarunsa 41 ne.

Minala ya ce "Na karanta abinda shafin senego.net ya rubuta, kuma karya ce tsagwaro aka yi min game da shekaru na".

Minala ya koma Lazio ne a karshen kakar wasan da ta wuce kuma ya taka leda tare da tawagar matasanta.