Igesund zai ci gaba da kocin Afirka ta kudu

Gordon Igesund Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin ya sha fama da kalu bale bayan kofin Afirka

Hukumar kwallon kafar Afirka ta kudu na goyon bayan Gordon Igesund kan yaci gaba da kocin tawagar kasar.

An dade ana rade-radi a kafafen yada labarai cewa za a sallame shi bisa kasa tabuka rawar gani da yayi a kofin Afirka ta 'yan wasa dake taka leda a gida.

Afirka ta kudu ce da ta karbi bakuncin gasar kofin Afirka amma ta kasa kai wasan zagaye na biyu.

Bayan da aka cire su a gasar, ministan wasanni na kasar Fikile Mbalula ya kira tawagar 'yan wasan da tarin tsintsiya ba shara.

A taron da kwamitin tsare-tsare na hukumar kwallon kafar kasar da ya gabatar ranar Alhamis ya tabbabata da Igesund zai ci gaba da horas da tawagar Afirka ta kudu.

Gobe ne Igesund zai sanar da sunayen 'yan wasan da za su kara a wasan sada zumunci da Brazil ranar 5 ga watan Maris a Johannesburg.