Zai yi wuya Cole ya buga Brazil 2014

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Roy Hodgson da Ashley Cole ranr da ya buga wa Ingila wasa na 100.

Kocin Ingila Roy Hodgson ya ce zai yi wuya dan bayan Chelsea Ashley Cole ya samu gurbi a cikin 'yan wasa 11 na farko da za su buga wa kasar gasar cin kofin duniya ta bana.

Cole mai shekaru 33 bai samu buga wa Chelsea wasa akai akai a bana ba, yayin da Leighton Baines na Everton ke neman take lambarsa a kungiyar kwallon kafa ta Ingila.

Hogson ya ce "An dade mutane na zaman canjin Ashley, yanzu kuma lokacinsa ne na bai wa wasu dama."

Kocin ya kuma musanta batun da ake yi cewa John Terry na Chelsea zai sake buga wa Ingila wasa bayan da ya yi ritaya a Satumban 2012.