'Wenger ya kware wajen rashin nasara'

Image caption Mourinho da Wenger na cacakar baki

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce Arsene Wenger na Arsenal "kwararre ne wajen rashin nasara".

Mourinho ya maida martani ne game da ikirarin kocin Arsenal a kan cewar Chelsea na tsoron rashin nasara, shi yasa kungiyar ba ta batun lashe gasar Premier ta bana.

Chelsea ce kan gaba a saman teburin gasar Premier a halin yanzu, inda ta dara Arsenal da maki daya.

Mourinho yace " Ya kware wajen rashin samun nasara, idan na shafe shekaru takwas babu kofi, zan bar Chelsea".

Tun shekara ta 2005 rabon da Arsenal ta lashe kofi.

Mourinho a lokacin da ya jagoranci Chelsea daga 2004 zuwa 2007, ya lashe kofin gasar Premier sau biyu. Sannan kuma ya lashe kofin gasar zakarun Turai tare da Porto da Inter Milan.

Karin bayani