FA: Manchester City da Wigan

wigan ManCity Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Manchester City za su kara da Wigan a kofin FA

Wigan mai rike da kofin FA za ta ziyarci filin Ettihad domin karawa da Mancheter City a wasan daf dana kusa da karshe.

Kungiyoyin biyu dai sun kara a bara a wasan karshe a Wembley, inda Wigan ta lashe kofin bayan data doke City da ci daya mai ban Haushi.

Everton wacce ta doke Swansea da ci 3-1, za ta ziyarci Emirates domin karawa da Arsenal.

Sauran wasanni sun hada a karawa a duk wanda ya doke wani tsakanin Sheffield Wednesday da Charlton, bayan da Sheffield United ta doke Nottingham Forest da ci 3-1.

Sunderland karkashin koci Gus Poyet na jiran kungiyar da zai kara da ita da zarar an kammala wasa tsakanin Brighton ko Hull.

Kungiyoyin za su kara a wasan daf dana kusa da karshe ne ranar 8-9 ga watan Maris.