Fulham ta dauki koci Felix Magath

Felix Magath
Image caption Kocin Jamus na farko da zai horas a gasar Premier

Fulham ta maye gurbin kocinta data kora Rene Meulensteen ta kuma maye gurbinsa da tsohon kocin Bayern Munich Felix Magath.

Meulensteen dan Holland wanda ya gaji Martin Jol da aka sallama a Disamba, ya shaidawa BBC cewa an sallame shi aiki amma kwantiraginsa na nan da Fulham.

Shugaban Fulham Shahid Khan ya ce "Saura wasanni 12 a kammala Premier kakar wasan bana, baza mu amince da rashin kyakkwawan sakamako ba. Muna bukatar sauya matsayin da muka tsinci kan mu da gaggawa.

Magath, mai shekaru 60, ya rattaba kwantiragin watanni 18 a Fulham wacce take matsayi na karshe a teburin Premier. Ya lashe kofin Bundesliga na Jamus karo uku, na baya bayan nan shi ne wanda ya dauka da kungiyar Wolfsburg a shekarar 2009, shi ne kuma dan Jamus na farko da zai Horas a gasar Premier.