Najeriya za ta kara da Girka da Amurka

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Najeriya na shirin ganin ta taka rawar gani a Brazil a bana

Najeriya za ta kara a wasannin sada zumunci da Girka da Amurka a watan Yuni, a shirye- shiryen da take na tunkarar kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci a bana.

Zakarar Afirka za ta fara fafatawa da Girka a Philadelphia ranar 3 ga watan Yuni, sannan ta buga da Amurka a Jacksonville, Florida ranar 7 ga watan Yuni.

Wasannin na daga cikin shirin da Super Eagles take na atisaye a Amurka kafin ta karasa Brazil domin buga kofin duniya.

Hukumar kwallon kafar Najeriya (NFF) na fatan hada wasan sada zumunci a gida a watan Mayu kafin tawagar ta koma Amurka domin yin atisaye.

Najeriya za ta kara da Mexico a Atlanta, Georgia ranar 5 ga watan Maris a inda ake fatan koci Stephen Keshi zai gayyato karin 'yan wasa domin su nuna hazakarsu.

Halartar kofin duniya da Najeriya za tayi a Brazil shi ne karo na biyr da kasar ke hakartar kofin duniya.