Bama tsoron zuwa Emirates - Martinez

Roberto Martinez Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Martinez ne ke rike da kofin FA, wanda ya lashe da Wigan a bara

Kocin Everton Roberto Martinez ya ce baya tsoron karawa da Arsenal a filin Emirates a wasan daf dana kusa da karshe na gasar FA, bayan da suka doke Swansea City da ci 3-1.

'Yan wasan Everton Lacina Traore da Steven Naismith da kuma Leighton Baines ne dai suka zura kwallayen a Goodison Park da ya ba ta damar kaiwa wasan daf dana kusa da karshe.

Martinez ya ce "Mun so ace a gida za mu karbi bakuncin su, amma duk daya ne - idan har kana son lashe kofi sai ka shirya haduwa da kowacce kungiya."

Martinez dan Spain a lokacin da yake horas da Wigan ya doke Manchester City a bara, ya kuma kara da cewa "Idan har ana son ganin kwazonka a kofin kalubale sai ka nuna kwarewar ka".