Manchester City ta dara United - Pellegrini

Manuel Pellegrini Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kocin ya auna kokarin City fiye da United a kakar bana

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya ce kungiyarsa ce ke kokari a birnin Manchester a kakar wasa ta bana, a shirin da suke na karbar bakuncin Barcelona a zagaye na biyu na gasar zakarun Turai.

Pellegrini dan Chile ya kara da cewa ba zai manta da nasarorin da United ta samu a baya ba, amma sakamakon nasarorin da City ke samu a kakar bana ta dara abokiyar hamayyarta.

Kocin ya ce "Matsawar za a kwatanta kokarin da muke yi a bana to lallai babu wata kungiya a Manchester da ta wuce City."

"Sai dai ba za mu manta da kokarin da United ta yi a baya ba. Muna ta harin lashe kofuna da dama - ba kawai na gida ba har dana nahiyar Turai da duniya gabaki daya", in ji Pellegrini.

City tana matsayi na uku a teburin Premier da tazarar maki uku tsakaninta da Chelsea mai matsati na daya a Teburi amma da kwantan wasa daya.