'City za ta kara da raunan nar Barcelona'

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin ya ce Barcelonan wannan lokacin bata baya bace

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce Manchester City za ta kara da raunan nar Barcelona a wasan zagaye na biyu na gasar kofin zakarun Turai.

Barca ta lashe kofin a shekarun 2009 da 2011 tun daga lokacin ta kasa kaiwa wasan daf dana karshe.

Mourinho tsohon kocin Real Madrid ya ce "Manchester City ce take da damar lashe wasan da za su kara."

Dan kwallon Barcelona mai tsaron baya Gerrad Pique ya ce kungiyarsa ta rasa kwarjinin da take da shi.

Mourinho wanda ya yi aiki da Barcelona karkashin marigayi Sir Bobby Robson, yana da rashin jituwa da tsohuwar kungiyarsa abinda yasa yake kokarin kawo rudani kafin a kara a wasan.

Kocin ya shaidawa ITV cewa Barcelona ake ganin za ta lashe wasan, amma Barcelonar bana ba wacce aka sani bace a shekarun baya.