Dike ba zai bugawa Nigeria wasa ba

Bright Dike
Image caption Dan wasan zai yi jinya har bayan gasar kofin duniya

Dan wasan Nigeria Bright Dike mai zura kwallo a raga ya ji raunin da zai yi jinya har bayan gasar kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci.

Dike mai shekaru 27 ya ji raunin ciwon agara karo na biyu kenan a cikin shekaru uku a lokacin da yake atisaye da kungiyarsa ta Toronto ranar Litinin.

Dan wasan na cikin tawagar Nigeria da za ta kara da Mexico a wasan sada zumunci a ranar 5 da Maris.

Dike ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa "Ranar Litinin ita ce bakar ranar da bazai manta da ita a rayuwarsa ba".

Hukumar Kwallon kafar Nigeria - NFF ta ce raunin da Dike ya ji abin takaici ne ga tawagar 'yan wasan Super Eagles.