Barcelona ta rasa kwarjinin ta- Pique

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Barcelona ta lashe gasar Champions League a 2009 da 2011

Dan wasan bayan kulab din Barcelona Gerard Pique ya ce maiyiwuwa ‘yan wasan su yanzu sun rasa kwarjinin su, gabanin karawar da zasu yi da Manchester City a gasar Champions League.

Barcelona ta lashe wannan gasa a shekarar 2009 da kuma 2011 amma ta kasa kai labari zuwa wasan kusa dana karshe tuni.

Tsohon dan wasan Manchester United Pique ya ce maiyiwuwa basa tsoron mu kamar da shi yasa a shekaru biyun da suka wuce bamu lashe gasar Champions League ba.

Amma ya ce ‘’duk da daka zamu iya yin fice amma dole ne mu nunawa duniya cewa zamu iya’’.